Monday, 8 October 2018

Kada Ku Damu Da Abinda 'Yan Adawa Za Su Ce>>Sule Lamido Ga Magoya Bayansa

Ga abinda Sule Lamido ya ce "haka Allah ya kaddara saboda haka ina kira ga magoya bayana da ku kasance masu godewa Allah a duk halin da kuka tsinci kanku domin shi lamarin Allah ba' a fushi da shi.


Ya kuma kara da cewa "mu dauki kaddara mu marawa Atiku Abubakar baya tunda shi Allah ya zaba, bawai muyi fushi da zabin Allah ba

Ya kuma gargadi magoya bayansa da kada kowa ya biyewa abinda 'yan adawa zasu fada koyi posting akan rashin nasararsa domin shi da Atiku duk mutane daya ne tunda dukkansu yayan jam'iyar PDP ne

Ya kuma yi fatan Allah ya bawa Atiku Abubakar nasara a zaben 2019 da ma sauran 'yan takarkari na jam'iyar PDP baki daya.
Rariya.

No comments:

Post a Comment