Sunday, 21 October 2018

Kada ku yi zagi: ku yi magana da hujja>>Atiku ya gayawa masoyanshi

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP,Atiku Abubakar yayi kira ga masoyanshi da cewa kada su biye a yi zage-zage dasu, za'a musu barazana, karya da kalaman kiyayya amma kada su damu su kawar da kai su maida hankali kan aikin sake gina Najeriya.Ya kara da cewa maimakon zagi, su rika magana da hujja. Mu yi aiki tare dan ciyar da Najeriya gaba.

No comments:

Post a Comment