Wednesday, 24 October 2018

Kalli abinda ya wakana tsakanin Ronaldo da wani da yayi kutse a wasansu da Man U da ya sanya Mourinho dariya

Ana tsaka da wasan gasar cin kofin zakarun turai tsakanin kungiyoyin Juventus da Manchester United a daren jiya sai ga wani da yayi kutse ya runtuma da gudu ya shiga filin dan ya gana da Ronaldo.Saidai hakanshi bai cimma ruwa ba, domin kamin yaje gurin Ronaldon, masu aiki a filin wasan sun isa kanshi inda suka tumurmusheshi a kasa zasu fita waje dashi.

Da yaga haka sai ya daga hannu sama ya kwalawa Ronaldo kira, aikuwa Ronaldon sai ya matso kusa dashi ya mika mishi hannu suka gaisa sannan ya gaya mishi wasu kalami da ba'a rahoto su ba.

A yayin da hakan ke faruwa, kyamara ta nuno me horas da 'yan wasan Man U, Jose Mourinho yana kyalkyala dariya.

No comments:

Post a Comment