Sunday, 7 October 2018

Kalli hoton da sallau ya saka shi da Furera: Yace rayuwa wucewa take kamar ba'a yi ba

A wallafar karshe ta mulajjar fim, cikin manyan kanun labaranta da suka dauki hankula sosai akwai labarin mutuwar auren taurarin shirin fim din nan na tashar Arewa24 watau Dadin Kowa, Umar Jigirya wanda akafi Sani da Sallau da matarshi, Amina Sani Muhammad wadda aka fi sani da Furera.


Da yawan masoya wadannan jarumai sun yi alhinin jin cewa auren ya mutu.

Saidai a wani yanayi me sarkakkiya, Umar watau Sallau, ya wallafa wannan hoton na Furera inda ya rubuta a jikinshi cewa, Rayuwa wucewa take kamar ba'a yiba.

Wannan abu dai ya saka alamar tambaya a zukatan masoyanshi, yayin da wasu ke ganin cewa hoton be dace ba wasu kuwa tambaya suke ina maganar cewa auren su ya mutu?

Wata tambayar da zata zo zuciyar mutum itace, ko kuwa dai Sallau din yana kewar tsohuwar  matar tashi ce?

Koma dai menene mudai daga nan zamu ce muna musu fatan Alheri.

No comments:

Post a Comment