Wednesday, 24 October 2018

Kalli hotunan gadar China mafi tsawo da tsada Duniya

Wadannan hotunan gadar kasar China ce wadda masana suka bayyana ta a matsayin mafi tsada da kuma tsawo a Duniya, nan bada dadewa ba jama'ar kasar zasu fara amfana da ita.

Kasar ta China tace dan girgizar kasa ko kuma ambaliyar ruwa babu abinda za su wa wannan gada, an kuma ginata ta yanda jiragen ruwa zasu iya wucewa ta karkashinta ba tare da wata matsala ba.

Haka kuma sanadiyyar wannan gada an kirkiri tsiburai na shakatawa ga masu yawon bude ido.
No comments:

Post a Comment