Friday, 5 October 2018

Kalli ma'aikacin baiwa jirgi hannu da ana tsaka da girgizar kasa a Indonesia amma sai da ya gama baiwa wani jirgi da ya zo tashi hannu, ya tashi lafiya amma shi ya rasa ranshi

Yau sati guda kenan da faruwar girgizar kasar da aka yi a Indonesia wadda ta yi sanadin tsunami, ruwa me karfin tsiya ya shiga cikin birnin Palu na kasar yayi banna sosai wanda zuwa yanzu gawarwakin da aka samu sun haura 1500.Labarin wannan matshin ma'aikacin filin jirgin sama dake baiwa jirgi hannu wajan sauka da tashi ya taba zukatan mutane sosai, matashin da shekaru 22 da haihuwa me suna Anthonius Gunawan Agungu ya na daidai kan wata hasumiya inda dama daga nanne yake baiwa jirgi hannu sai aka fara girgizar kasa.
A daidai lokacin kuma wani jirgi ya zo tashi, sai da Agung ya tsaya ya baiwa wannan jirgi hannu ya tashi sama sannan shi kuma yayi tsalle daga kan hasumiyar da yake dake shirin rugujewa saboda tsananin girgizar kasa, faduwar da yayi ya samu karaya da mummunan raunuka kamar yanda Buzzfeed ta ruwaito.
Ana kan hanyar kaishi asibiti ya mutu. Mutane sun yaba da wannan jarumta da ya nuna.


No comments:

Post a Comment