Sunday, 28 October 2018

Kalli wani sabon salon fariya da ya shigo Duniya, Zaka rike baki

Duniya kullun sai sabbin abubuwa ke fitowa, wasu masu ma'ana wasu kuma ka rasa ma menene manufarsu. Wani sabon salon fariyane ya fito a kasar China wanda 'ya'yan masu kudi ke nuna irin abubuwa masu tsada da suka mallaka.


Abin ana mishi lakabi da Flaunt your wealth ko kuma falling Stars a turance inda suke amfani da kafefen sadarwa na zamani na Weibo wanda shine daya daga cikin wanda suka yi fice a kasar Chinan da kuma shafin Instagram.

Yanda ake yinshi shine mutum zai samu gefen titi, inda mutane ke wucewa a kasa, ya bude motarshi ta alfarma ya zuba kayayyaki masu tsada, jaka ta Gucci da kayan kwalliya  ko kuma kudi, Agogo, Takalma dadai sauransu a kasa.
Saidai a kasar ta China an samu wasu mutane biyu da suka yi irin wannan abu a gefen titi da ya jawo cinkoson ababen hawa da mutane sosai, saboda 'ya'yan hamshakan masu kudi ne babu me iya musu magana, saidai 'yan sanda sun kamasu an ci su tara da takai sama da dala 20.

Saidai da bin yayi yawa, ma'aikatan gwamnati, Likitoci, sojoji, da sauransu hadda talakawa ma bayin Allah duk sun shiga ana damawa da su, inda suke kwanciya kusa da takardun aiki da bindigogi da kayan miya dadai sauransu.

Wannan abu ya samo asali ne daga kasar Rasha amma yanzu ya zama ruwan dare a kasar China kuma ya dauki hankulan mutanen kasar sosai.

Anan zaku ga wasu daga cikin hotunan yanda abin ya kasance:


1 comment:

  1. Tabdijam! Hakika idan mutum yana duniya baigama jin ko ganin abubuwan mamaki ba, muna fatan ALLAHU SWT yasa mugama da wannan rayuwar ta duniya lafiya amin.

    ReplyDelete