Friday, 5 October 2018

Kalli yanda akayi gumurzu tsakanin 'yan PDP masu zanga-zanga da 'yansanda

A yau, Juma'ane shuwagabannin PDP suka gudanar da zanga-zanga a Abuja inda suke adawa da sakamakon zaben jihar Osun da suke zargin jam'iyya me mulki APC ta yi murdiya saidai zanga-zangar bata kare da dadi ba domin kuwa a lokacin da suka je hedikwatar 'yansanda, masu zanga-zangar sun gamu da tirjiya.Dalilin wannan hatsaniya, an samu tsaikon ababen hawa a titin Shehu Sahagari  inda masu zanga-zangar suka tare hanya.

Wannan na daya daga cikin dalilan da yasa 'yansandan suka fitar da sanarwar gayyatar sanatocin da suka yi gaba-gaba a wannan zanga-zanga dan yin bayani.


No comments:

Post a Comment