Friday, 19 October 2018

Kalli yanda ake karawa mara lafiya ruwa a Kebbi: Saidai gwamnatin jihar ta musanta haka

A wannan hoton an nuna yanda ake amfani da icce wajan rataya ruwan da ake wa mara lafiya karin ruwa dashi kuma rahotanni da dama daga kaffen sadarwa na Internet sun nuna cewa a jihar Kebbi, garin Zuru ne wannan abu ya faru.Wani shafi me suna, West Africa Reporters ya wallafa wannan labari.

Saidai gwamnatin jihar Kebbi ta mayar mishi da martanin cewa, nan fa ba Kebbi bane. Ku aika ma'aikacinku.

Shafin ya fadi cewa ba ya wallafa labari sai ya tantanceshi dan haka yana shawartar gwamnan da ya aika da wakilanshi su tabbatar da wannan lamari ko kuma a musu bincike akan sahihancin hoton.

No comments:

Post a Comment