Thursday, 25 October 2018

Kalli yanda makiyaya suka cika birnin Madrid na kasar Sifaniya da dabbobinsu a wani bikin da aka yi

Wadannan hotunan wasu makiyayane da suka shiga birnin Madrid na kasar Andulus, sun shiga garinne a matsayin wani biki da ake yi duk shekara na tunawa da hijirar da makiyaya ke yi da dabbobinsu a zamanin da kamin kasar ta ci gaba haka.Makiyayan da suka fito daga yankunan karkara sun bi hanyoyin da iyaye da kakanni suka bi a da na cikin birnin yayin wannan hijira da suke yi da dabbobin nasu a shekarun baya.

Jama'ar gari sun fito suna kallo don nishadi.
Buzzfeed.


No comments:

Post a Comment