Saturday, 6 October 2018

Kalli yanda wani direba ya sakarwa Biri tukin mota cike da fasinja

Wannan wani dire ba ne a kasar India dake tukin motar Bas ta fasinja, an ganshi ya sakarwa wani biri sitiyarin motar yana juyashi yayin da shi kuma yake sarrafa birki da total.


Rahotanni sunce birin na wani fasinja ne dake cikin motar amma fa fasinjojin sun nuna tashin hankalinsu akan wannan lamari.

An ruwaito cewa, jami'an kasar ta India na tuhumar direban da saka rayuwar mutane cikin hadari.

No comments:

Post a Comment