Thursday, 25 October 2018

Kar ka koma APC amma in kaki ji ba kaki gani ba>>Sanata Shehu Sani ya gargadi Ekweremadu

Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani daya fice daga jam'iyyar APC zuwa PRP bayan da jam'iyyar APC din ta hanashi tikitin takara, ya fito ya gargadi abokin aikinshi, mataimakin kakakin majalisar dattijai, Ike Ekweremadu akan rade-radin da ake na cewa zai koma APC din.


Sanata Shehu Sani ya bayyana ta shafinshi na dandalin Twitter cewa, dan uwa Ike, ka tsaya a inda kake ya fi maka, ni dai  na fita, in kuma kaki ji ba kaki gani ba.
Saidai tuni rahotanni suka bayyana cewa, Ekweremadu ya karyata cewa zai koma APC.

No comments:

Post a Comment