Sunday, 28 October 2018

Kar mu yi tsammanin za mu ci mulki ko da da magudi idan bamu gyara kurakuran mu ba>>Bukar Abba Ibrahin ga APC

Dan majalisar tarayya kuma jigo a jam'iyyar APC, Bukar Abba Ibrahim ya gargadi jam'iyyar tashi da cewa kada fa su zauna suna tsammanin zasu samu nasara irin wadda suka samu a zaben shekarar 2015.


Bukar ya bayyana hakane a wajan kaddamar da littafinshi me suna Poorlitics a babban birnin tarayya, Abuja, kamar yanda jaridar Independent ta ruwaito.

Yace gwamnatin su ta APC bata yi abinda ake tsammaninta da yi ba kuma bata da banbanci da PDP da suke kokarin kawarwa, Bukar yace idan fa basu tashi tsaye ba suka yi aiki tukuru suka kuma canja salo to tabbas zasu sha mamaki a zaben 2019 domin duk wani magudi da zasu yi ba zai sa su yi nasara ba.

Ya bayar da shawara ga gwamnati inda yace ya kamata a saki mutanen da ake tsare da su saboda siyasa da kuma maganar yaki da cin hanci da rashawa ya kamata ya shafi duk wanda aka kama ne bawai wasu zababbun mutane ba ta yanda ba zai zama kamar bita da kulli ne.

Ya kara da cewa irin tsare-tsaren da gwamnatin APC ta dauka ne fa ya gurgunta tattalin arzikin kasarnan kuma sai sun gyara sannan za'a ga canji.

Bukar ya karfafawa matasa gwiwar karanta littafin nashi inda yace a ciki zasu karanta dabarar da zasu yi amfani da ita wajan kwace mulki daga hannun tsaffin da suka yi kane-kane a harkar mulkin kasarnan.

No comments:

Post a Comment