Monday, 8 October 2018

Karanta abinda Atiku yawa gwamnan jihar Rivers bayan da ya nuna rashin jin dadin nasarar da ya samu

Rahotanni sun bayyana cewa, bayan kammala zaben fiida gwanin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP wanda Alhaji Atiku Abubakar ya lashe aka kuma sanar da sakamakon zabe, gwamnan Jihar Rivers, Nyesome Wike ya fice daga filin taron rai a bace.

Majiyoyi daban-daban sun ruwaito cewa, Wike da wasu manya a jam'iyyar sun goyi bayan gwamnan jihar Sakkwatone, Aminu Waziri Tambuwal a wannan zabe da aka yi, ana ganin irin goyon bayan da ya samu daga su ne ma har ta kai ga ya zo na biyu.

Da bai samu nasara ba, wadanda suka goya mai baya basu ji dadi ba.

Amma duk da Wike din ya fita daga filin Ranshi a bace, Atiku ya bishi har gida ya gaisheshi.No comments:

Post a Comment