Friday, 12 October 2018

Karanta Abinda Fati Muhammad tace akan Atiku

Tun bayan da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bar jam'iyya me mulki ta APC zuwa tsohuwar jam'iyyarshi ta PDP har ma ya lashe zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa, cece-kuce sai kara shiga yake tsakanin APC da Atiku inda suke jifar juna da kalamai.


Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Fati Muhammad na daya daga cikin masu yiwa Atikun Kampen zama shugaban kasa kuma ga abinda tace akan abinda ke faruwa tsakanin Atikun da APC,kamar yanda Rariya ta ruwaito.

RA'AYIN Fati Muhammad

 "A lokacin da Atiku yake APC ba maciyin rashawa bane. A lokacin da Buhari ya yi amfani da jirgin Atiku domin yin yakin neman zaben 2015, ba a kira shi maciyin rashawa ba. Lokacin da Atiku ya bada gudummawar kudi a nasarar da APC ta yi zaben 2015, nan ma ba a kira shi maciyin rashawa ba. Amma Atiku na barin APC sai ya zama maciyin rashawa".

No comments:

Post a Comment