Tuesday, 2 October 2018

Karanta Abinda matar aure 'yar Arewa ba zata taba iya yiwa mijinta ba

Wata baiwar Allah me amfani da shafin yanar gizo na Twitter ta bayyana abubuwan da matar Aure 'yar Arewa ba zata taba iya yiwa mijinta ba.


Ta fara da cewa, matar aure 'yar Arewa ba zata taba fallasa mijinta ba koda ta kamashi da cin amanarta. Haka kuma ba zata taba fallasa hotunan batsa na budurwar da mijin nata ke cin amanarta da ita ba. Matar aure 'yar Arewa ta musammance kuma tana da hakuri.

A wasu yankunan Najeriya dai akan samu wasu lokutan da matan aure ke fallasa hotunan batsa da 'yan mata ke turawa mazajensu a shafukan sada zumunta.

No comments:

Post a Comment