Monday, 8 October 2018

Karanta Abinda Saraki yace bayan da ya sha kaye

Bayan da ya sha kaye a zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, kakakin majalisar dattijai, Bukola Saraki ya taya Atiku murna inda ya bayyana cewa zasu yi aiki tare dan samun nasarar jam'iyyarsu.


Saraki yace dama can sun san cewa mutum daya ne zai lashe wannan zabe dan haka a madadin sauran 'yan takara yana taya Atiku Murna kuma zasu yi aiki tare dan tabbatar da cewa yayi nasara.

No comments:

Post a Comment