Sunday, 14 October 2018

Karanta alkawarin mukamin da Atiku yawa Yarbawa idan suka zabeshi shugaban kasa

Tun kamin ganawar dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo an samu rahotanni cewa Atikun zai dauki mataimakinshi ko dai daga yankin Inyamurai ko kuma daga yankin yarbawan.


Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa bayan da Atikun ya dauko Peter Obi a matsayin mataimakinshi daga yankin inyamurai sai kuma yawa yarbawa Alkawarin mukamin sakataren gwamnati idan suka zabeshi.

Rahoton yace mukamin mataimakin shugaban kasa na yanzu da Osinbajo ke rike dashi be tsinanawa yankin yarbawan wani abin azo a gani ba kamar yanda wasu masu ruwa da tsaki na yankin ke fadi, domin kuwa yawancin ayyukan da aka yi a yankin dama can na tsohon shugaban kasa, Jonathan ne.

Dan haka suke ga gara yanzu su yi tafiya tare da Atikun.

Rahoton ya kara da cewa mukamin sakataren gwamnatin tarayya daidai yake da mukamin mataimakin shugaban kasa idan ma bai fishi ba idan aka yi la'akari da manyan ayyukan dake karkashinshi.

No comments:

Post a Comment