Sunday, 14 October 2018

Karanta alkawurran da Saraki yawa 'yan majalisun APC dan kada su saukeshi

Tun kafin majalisar dattijai ta dawo daga hutun da ta tafi a cikin satin da ya kare batun tsige shugaban majalisar Bukola Saraki ya ke cigaba da yawo a kafen yada labarai.

Sai sai wani abun mamaki shine yadda sanatoci da shugabannin jam'iyyar APC da ke yunkurin tsige Saraki su ka yi shiru da wannan magana bayan dawowa daga hutunta ranar Talata.

Wani rahoton bincike da tuntuba da jaridar The Cable ta wallafa ya bayyana yadda Saraki ya cimma yarjejeniya da mambobin APC a majalisar dattijai a kan batun na tsige shi ta hanyar amincewa da wasu sharudai.

Daga cikin sharudan akwai batun zartar da duk wasu kudiri da shugaba Buhari ya aiko kuma har yanzu majalisar ba ta sahale ma su ba da kuma amincewa da dukkan jama'ar da Buhari ya aiko domin majalisar ta tantance su.
Alamun hakan sun fara tabbata ne bayan majalisar ta amince da batun kasafin kudin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da shugaba Buhari ya gabatar wa majalisar.

Kazalika majalisar ta amince da nadin dukkan kwamishinonin hukumar kidaya (NPC) 20 da nadin mataimakin gwamnan babban bankin kasa (CBN), Folashodun Shonubi, da Buhari ya turawa majalisar dattijai.

Shugaba Buhari ya mika kudiri 15 ga majalisar dattijai tun bayan hawansa mulkin a 2015 amma 5 ne kawai su ka samu sahalewar majalisar ta dattijai.

Bayan batun amincewa da kudiri da tantance wadanda za a bawa mukami, an cimma yarjejeniya tsakanin Saraki da mambobin APC kan cewar za a bawa batun da ya shafi cigaban kasa fifiko tare da jingine banbancin jam'iyya.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment