Friday, 26 October 2018

Karanta amsar da Nafisa Abdullahi ta baiwa wani da yace mata inama ace katin gayyatar aurenki ne kike yadawa haka

Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi na ci gaba da tallata sabon fim dinta na Yaki a Soyayya saidai kamar yanda muka ji a farkon makonnan wani ma ya sake takalo mata maganar aure.


Mutumin yace, inama ace katin gayyatar aurenki ne kike yadawa haka da ya fiye maki Alheri. Allah yasa mu gama da Duniya lafiya.

Saidai shima kamar na farkon, Nafisar bata dauka da zafi ba ta bashi amsar cewa, je ka kalli Yaki a Soyayya.

No comments:

Post a Comment