Saturday, 27 October 2018

Karanta yanda ta wakana tsakanin Da da Uba da suka hadu a shafin Twitter

Wani lamari daya faru tsakanin tsohon dan takarar gwamnan jihar Zamfara, Dr. Bello Matawallen Maradun da danshi, Dogo Bello a dandalin Twitter ya dauki hankulan dubban mutane a ciki da wajen kasarnan.


A lokuta da dama matasa sukan bayyana cewa ba zasu so iyayensu su shigo shafukan sada zumuntar da suke amfani da su ba, wasu kuma zaka ji suna fadin mahaifan nasu sun aiko musu da sakon zama abokai amma sun ki amincewa.

Irin hakane ya faru da Bello da danshi.

Dan na Bello ya rubuta cewa, watau babana dai yana shafin Twitter yanzu.. hmmm.

Bellon ya mayarwa da danshi martanin cewa, Eh ina nan, ka rufe shafinka na Instagram(saboda ni) wannan ma zaka rufeshine?
Wannan lamari ya matukar dauki hankulan mutane sosai.

No comments:

Post a Comment