Sunday, 7 October 2018

Karanta yawan kudin da 'yan PDP suka raba a gurin zaben fidda gwani shugaban kasa

Da alama wakilan jam'iyyar PDP da suka yi zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa da ya gudana a jihar Rivers sun dara sosai saboda irin makudan kudaden da aka ruwaito 'yan takara sun basu.


Jaridar Punch ta ruwaito cewa kowane wakili ya samu dalar amurka 9000, kimanin sama da naira miliyan 3 kenan, banda wanda aka basu a boye. Haka kuma an ruwaito cewa kimanin wakilai 4000 ne suka kada kuri'a a wajan zaben.

Idan aka lissafa za'a ga an kashe dala miliyan 36 kenan wanda a kudin Najeriya kimanin sama da Naira miliyan dubu 11 kenan.

Wasu daga cikin wakilan sun bayyana cewa suna fatan dama ace a sake wannan zabe dan kuwa sunji dadin abinda suka samu.

No comments:

Post a Comment