Wednesday, 17 October 2018

Karbar kudi a hannun 'yan kwangila ba sabon abu bane, kawai an so a batawa Ganduje sunane>>Wani kwamishinan Kano ya kare Gwamnan

Kwamishinan ci gaban kauyuka da gundumomi na jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso ya kare gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje akan bidiyon da aka nunashi yana karbar daloli wanda aka yi zargin cewa na cin hancine da 'yan kwangila suka bashi.

Kwamishinan yace, karbar kashi 15 zuwa 25 cikin dari na kudin kwagila a aikin gwamnati tun daga kan gwamnatin tarayya har zuwa jiha ba sabon abubane, kowa ya san da haka, duk da dai yin hakan baya kan doka.

Ya kara da cewa, yana kalubalantar 'yan kwangilar da su fito su gayawa Duniya cewa ba'a basu kwangilar ba sai da suka yadda su bayar da kashi 15 ko kashi 25, yace me yasa tun tuni basu fito da wannan bidiyo ba sai yanzu?

Yace, karbar irin wadannan kudi a aikin kwangila ba sabon abu bane kawaidai ana so a batawa gwamnan sunane.

Kuma ya kara da cewa bidiyon ma da aka fito dashi na bogi ne idan suka ga dama su ta fito da bidiyon har guda dubu sai mene?

Ya kara da cewa kuma ba Ganduje kadai aka tabawa wannan irin kasassababa akwai Ibrahim Shekarau da Jibrilla Bindow na Adamawa da sauransu duk an musu irin wannan abu.

Jaridar Daily Nigerian din ce dai ta ruwaito wannan kwamishina yana fadin wannan magana a wani shirin gidan radiyon Freedom ta Kano me suna, Jagoran Gwamnati a Karkara wanda aka watsa a ranar Lahadin data gabata.

No comments:

Post a Comment