Wednesday, 17 October 2018

Kasar da iyaye ke sayar da 'ya'yansu saboda tsananin talauci

A yayin da matsin tattalin arzikin Venezuela ke kara muni, an kiyasta cewa hauhawar farashi za ta kai kashi 1,000,000% zuwa karshen shekarar nan.

Yara da dama na ci gaba da gararamba a tituna, wasu iyayen kuma na yin kyauta da 'ya'yansu don gudun wahala.

A wani rahoto da BBChausa ta wallafa ta yi hira da wasu iyaye da suka bayar da 'ya'yansu saboda ba zasu iya ciyar dasu ba duk da dai cewa ba a son ransu suke yin hakan ba.

Wata da aka yi hira da ita ta bayyana cewa tana haihuwar jaririyarta ta bayar da ita kuma ta yi hakanne dan tana fatan diyartata ta samu kyakkyawar rayuwa amma tana sa ran nan gaba zata amso diyartata.

Haka kuma an yi hira da wasu yaran dake gararanba a kan tituna wanda suma suka baro gidajen iyayen nasu saboda babu abinci da kuma kuncin rayuwa.

No comments:

Post a Comment