Friday, 12 October 2018

Kasar Koriya ta kudu ta fara samar da audugar al'adar mata a bayukan al'umma kyauta

A wani salo na kawowa rayuwar kananan mata musamman wanda suka fito daga gidajen talakawa, kasar Koriya ta kudu ta fara samar da audugar da matan ke amfani da ita lokacin al'ada a bayikan cikin al'umma saboda kota kwana.


A shekarar 2016 wani rahoto ya bayyana cewa matasan mata da damane da suka fito daga gidajen iyaye talakawa basa iya sayen audugar lokacin da suke al'ada saboda tsadarta, maimakon haka saidai su rika amfani da shimfidar cikin takalmi kafa ciki, kamar yanda Buzzfeed ta ruwaito.

Kasar Koriya ta kudu dai na da audugar al'ada ta mata mafi tsada a nahiyar Asia.

No comments:

Post a Comment