Friday, 19 October 2018

Kashi 76 na al'ummar Najeriya ba su kai shekaru 25 ba>>rahoto

Wani rahoton hukumar kula da yawan jama’a na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa kashi 76 na al’ummar Najeriya na tsakanin shekarun 1 zuwa 24 ne a dai dai lokacin da yawan al’ummar kasar baki daya ke tasamma miliyan 195.9.


Cikin rahoton na Majalisar Dinkin Duniya wanda ta yiwa lakabi da damar zabin da al’umma ke da shi na haihuwa ko akasin haka, Majalisar ta bayyana cewa akwai akalla mutane miliyan 148.8 da ke tsakanin shekaru 25 zuwa kasa.

Sai dai kuma rahoton na Majalisar Dinkin Duniya na cin karo da na hukumar kula da yawan jama’a ta Najeriyar na baya-bayan nan wanda ke nuna cewa yawan al’ummar Najeriya a watan Aprilun 2018 ya kai miliyan 198.

Rahoton dai na zuwa ne a dai dai lokacin miliyoyin matasa a Najeriyar ke jibge ba tare da mahukunta sun samar musu ayyukan yi ba, yayinda wasu da dama kuma ke tsallakawa wasu kasashen don samun rayuwa mai inganci.

Haka zalika a Najeriyar akwai tarin kananan yara da basa samun damar karatu ciki kuwa har da 'ya'yan 'yan gudun hijirar wadanda suka rasa matsugunansu a yankin arewa maso gabashin kasar.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment