Monday, 22 October 2018

Kotu ta ki bayar da belin Ayo Fayose

Babbar kotun tarayya a jihar Legas ta ki bayar da belin tsohon Gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose kan tuhume-tuhumen cin hanci da rashawa da hukumar EFCC take yi masa.


Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati ta gurfanar da shi ne a ranar Litinin kan tuhume-tuhume 11 ciki har da laifukan cin hanci da rashawa da halarta kudin haram da sauransu.

Ana kuma zargin shi da karbar dala miliyan biyar daga hannun tsohon ministan tsaron kasar Musiliu Obanikoro, wanda ta ce ya yi amfani da su wajen yakin neman zaben gwamnan jihar a shekarar 2014.

Sai dai tsohon gwamnan ya musanta duka wadannan tuhume-tuhumen.

Fayose ya wallafa hotonsa lokacin da yake shiga kotun ta shafinsa na Twitter, inda ya ce yana da "tabbacin samun nasara."

Mista Fayose ya kai kansa ofishin hukumar EFCC ne jim kadan bayan ya mika mulki ga sabon Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi a ranar Litinin da ta gabata.

Kuma tun daga nan ne hukumar take ci gaba da tsare bisa tuhumarsa da laifin cin hanci da rashawa.

Fayose wanda ya yi gwamnan jihar Ekiti da ke kudancin Najeriya a karkashin jam'iyyar adawa ta PDP, yana yawan sukar manufofin gwamnatin Shugaba Buhari.

Bayan kotun ta ki amincewa da bukatar ba da belin shi, an umarce hukumar EFCC ta ci gaba da tsare tsohon gwamnan kuma daga nan an dage zaman har zuwa ranar Laraba mai zuwa.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment