Sunday, 28 October 2018

Ku daina zabar wanda basu da ilimi a matsayin shugabanni>>Sarkin Kano

Me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II ya gargadi 'yan Najeriya bisa zabar mutanen da basu da ilimi a matsayin shugabanni inda yace hakan yana da illa ga ci gaban kasarnan.


Sarkin yayi maganar nan ne jiya, Asabar gurin yaye daliban jami'ar Nile dake babban birnin tarayya, Abuja, kamar yanda The Nation ta ruwaito.

Sarkin yace a shekarun baya 'yan Najeriya sun zabi mutanen da basu da ilimi wanda hakan yayi sanadiyyar suma basu iya bayar da ilimi saboda basu san muhimmacinshi ba.

Yayi kira da a rika zabar mutane masu ilimi a matsayin shuwagabanni da kuma suma shuwagabanni su rika mayar da hankali wajan bayar da ilimi fiye da duk wani aiki da za'awa jama'a saboda gina al'umma shine abu mafi muhimmanci a kasa fiye da gina gadaje da titi, yayi kira da a yi amfani da kudin da ake bayar da tallafin mai wajan ilimantar da al'umma.

Sarkin ya kuma zargi shuwagabannin Arewa da rashin bayar da damar ilimi yanda ya kamata ga yara a yankin.

No comments:

Post a Comment