Saturday, 13 October 2018

Ku nemi zabin Allah kamin ku jefa kuri'arku>>Shugaba Buhari ga 'yan Najeriya

A yau, Asabarne aka gudanar da taron hadin kan addinai daban-daban dake Najeriya, wadanda suka samu halartar wannan taro sun hada da sarkin musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar na III da shugaban cocin kotolika ta Abuja John Cardinal Onaiyekan.Sauran wadanda suka samu halartar wannan taro akwai tsaffin shuwagabannin kasa, Abdulsalam Abubakar da Yakubu Gowon da dai sauransu.

A jawabinshi a gurin taron, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jawo hankalin malaman addinai da kada su saka kansu cikin harkokin siyasar bangaranci su kuma koyar da mabiyansu zaman lafiya da abokan zamansu, ta bangaren shuwagabannin al'umma kuma yayi kira a garesu da suma su dora mabiyansu akan hanyar da ta dace dan su zabi mutanen da suka dace a matsayin shuwagabanni a zaben 2019.

Shugaba Buhari ya kuma jawo hankalin masu zabe da su nemi zabin Allah kamin su je saka kuri'arsu.

Ta bangaren 'yan siyasa kuma yace, yanzu dai an kammala zabukan fitar da gwani dan haka yana kira a garesu da su amshi sakamakon da jam'iyyunsu suka fitar, wadanda kuma basu yadda ba yana kira a garesu da su bi hanyar da ta dace ta doka wajan neman hakkokinsu.

Shugaba Buhari yayi kira ga 'yan siyasar da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da rikon amana domin Allah zai tambayi yanda suka yi mulki.

No comments:

Post a Comment