Tuesday, 2 October 2018

Kuma dai: An sake gano wata motar Bas a rafin da aka gano motar sojan nan da ya bata a Jos

A rafin nan dai na jihar filato da aka gano motar sojannan da ya bata, Maj Gen. Idria Nur Alkali, an sake gano wata mota kirar Bas da direbanta a ciki.


Motar Bas din kirar Toyota ta bace ne tun ranar 24 ga watan Yuni da ya gabata kuma an ganota ne yau, Talata.

A cikin wannan rafi ne dai aka gano motar sojannan da aka yi garkuwa dashi aka kuma kashe watau, Maj Gen. Idria Nur Alkali.

No comments:

Post a Comment