Friday, 12 October 2018

Kun san dalilin da ya sa mata ke bukatar aiki a yayin haihuwa?

A cewar wani bincike da aka wallafa a mujallar kimiyya da The Lancet, yin aikin da ake yi wa mata yayin haihuwa a sassan duniya ya rubanya tun a shekara ta 2000.


Kididdiga ta nuna cewa daga shekara ta 2015, kaso 21 cikin 100 na haihuwar da aka yi aiki ake yi wa mata, kuma hakan ya karu da kaso 12 cikin 100 a shekara ta 2000.

Binciken ya kuma nuna cewa akwai bambamce-bambamce mai yawa a tsakanin kasashe masu arziki da marassa shi.

Ana yin aiki ne domin a ciro jariri a yayin haihuwa don a taimakawa matan da suka kasa haihuwa da kansu ko kuma suka samu wata matsala a yayin haihuwar, to amma kuma a wani lokaci a kan samu matsala a yayin wannan aiki.

Bukatar yi wa mata aiki yayin haihuwa ba ta wuce kaso 10 zuwa 15 cikin 100 na matan da ke haihuwa, to amma binciken da aka gudanar a kasashe 169, ya nuna cewa a zahirance a kan yi wa kaso daya cikin biyar na mata masu haihuwa aiki ne a yayin haihuwa, lamarin da masu binciken suka ce ya zamo babban abin damuwa.

Masu binciken sun ce mata a fiye da rabin kasashen duniya a yanzu, sun dogara ne a kan ayi musu aiki a haihuwa inda adadin ya fi yawa a kasashe kamar Jamhuriyar Dominican da Brazil da Masar da kuma Turkiyya inda kasasahen suka ce aikin da ake yi wa mata yayin haihuwa ya kai kaso 50 cikin 100.

To amma kuma ana samun karuwar yi wa mata aikin a yanzu a kudancin Asiya.

Wani abin kuma shi ne ba a fiye yi wa mata aiki yayin haihuwa ba a matalautan kasashe, kuma ko da a kasashen da suke matsakaita wajen samun kudaden shiga ma akwai wagegen gibi wajen yi wa mata aiki yayin haihuwa, inda sai dai mata masu hannu da shuni ne ke iya zuwa ayi musu aikin.

Masu binciken sun yi kira ga jami'an lafiya da mata da kuma iyalansu a kan su dai na zabar ayi musu aiki idan ba bukatar hakan ce ta taso ba, sannan kuma akwai bukatar kara wayar da kan mata game da illolin da yin aikin da ke da su.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment