Thursday, 25 October 2018

Kune zaku karbi mulkin Najeriya idan kuka zabi Buhari bayan ya gama>>Fashola ya gayawa yarbawa

Ministan gidaje, wuta da ayyuka, Babatunde Fashola ya ja hankalin 'yan uwanshi yarbawa da cewa idan fa su ka sake zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari a zaben 2019 to zabe na gaba bayerabene zai zama shugaban kasa.


Fashola ya bayyana hakane a gurin wani taro kan ayyukan raya kasa da ma'aikatar watsa labarai da al'adu da ta wayar da kan jama'a suka shirya a Legas wanda ya samu halartar ministan labarai, Lai Muhammad dana sufuri, Rotimi Amaechi dana ruwa, Sulaiman Adamu, kamar yanda Vanguard ta ruwaito.

Fashola yace banda ayyukan raya kasa da Buhari yake yi yanzu, yankin na Yarbawa zai samu damar yin shugabancin kasa nan da 2023 bayan Buhari ya gama mulkinshi wanda hakan yana bukatar su saka mishi kuri'arsu a zabe me zuwa.


No comments:

Post a Comment