Wednesday, 31 October 2018

Kungiyar tsaffin ma'aikatan sadarwa ta kasa ta godewa Buhari da biyansu hakkokinsu da yayi bayan da aka yi watsi dasu tun lokacin Obasanjo

Kungiyar tsaffin ma'aikatan kamfanin sadarwa na Najeriya, NITEL/MTEL sun godewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya dawo da biyansu hakkokinsu na barin aiki bayan da gwamnatin Obasanjo a shekarar 2006 ta tsayar da biyansu hakkokin nasu bayan sayar da kamfunan.


Kungiyar ta bayyana godiyar tata ce a cikin wata sanarwa data fitar a jaridun kasarnan ranar 29 ga watan October inda take godewa shugaba Buhari akan biyansu hakkokinsu da gwamnatinshi tayi suka kuma mai fatan alheri.

No comments:

Post a Comment