Saturday, 6 October 2018

Labarin wata mata da ta musulunta ta yi aure amma mijin ya wulakantata

Shin Sallah Muke Yi Ko Addinin Islama? 

Wannan baiwar Allah da kuke gani(a yi hakuri na zamu saka hoton ta ba)a tashar Mota muka hadu da ita ta fito daga gidan Surkuwanta jikin ta duk a jike, ta zo tashar mota tana kuka tana neman taimakon kudin mota zuwa Bauchi, bayan ta samu kudin motar shine ta shiga motar ta zauna a baya da 'ya'yanta guda biyu (Babbar ta Mace karamin na Miji). Babbar ko wando babu jikinta karamin kuma tsirara yake. 

A cikin motar mu Maza mu biyar ne sauran Mata,  amma kaf cikin Motan ba Wanda bai zubda hawaye ba,  sabila da halin da wannan Baiwar Allah ta tsinci kanta aciki. 

Kamar yadda ta zayyana mana cewa ita ba Musulma ba ce, Kirista ce, wacce take zaune da Iyayenta a wani Gari dake karkashin jihar Nasarwawa, a sanadiyyar wani Yaro dan Gombe ta Musulunta, domin nuna mata kauna da yayi,  ta rabu da Iyayenta a sanadiyyar sa, tabar Addininta a sanadiyar sa, ta rabu da kowa nata a sanadiyar sa, wanda yakai ga cewa Iyayenta sunyi mata gargadi inta kuskura wani abu yafaru tazo wajensu sai Sun kasheta, a taqaice dai Sun sallamata.

Suka yi Aure bayan ta musulunta,  Musulman dake garin Suka taimaka mata da kayan daki komi da komi suka zauna,  bayan tahaihu na farko Mace, tafara fiskantar rayuwa,  wulaqanci na yau daban na gobe daban,  ahaka ta haihu na biyu,  nanma yakwashe kayan dakin ya siyar, kaf allura bai bari ba, ga duka ba abinci babu sitirarar Yara da Nata,  gashi awajen dasuke babu Wanda ta sani ballantana ya taimake ta,  tafara zuwa makarantar Islamiya domin ta iya ibada sosai ya cireta yace karuwanci take zuwa, bayan haka ya saketa,  ya gudu, ta taso daga garin da suke bayan an kore ta a gidan haya,  ta tawo Gombe domin fadawa Mahaifiyar sa, ashe Mahaifiyar ma ita kam bata ma yarda da musuluncin yarinyar ba,  ta zazzageta ta kore ta, ta watsawa jikokinta da matan ruwan zafi,  bai samu yaran ba amma ya samu uwar. Shine ta ce ba ta ma san ina za ta je ba,  kawai ta zo tasha ne ta ji ana motar Bauchi,  shine ta ce bari ta shiga sisi bata da shi ga yara kamar Mahaukata ko kaya babu a jikin su, a nan aka hada mata dari takwas 800, ta shiga motar Bauchi. 

Abinda ya bani mamaki shine furucinta na karshe wacce take cewa "Miyasa na shiga Musulunci,  inda nasan haka Musulunci da Musulmi suke da ban shiga ba, na rabu da kowa na,  sabila da Musulunci, na rasa gatana sabila da Musulunci, na rasa komi sabila da Musulunci,  abinda Musulunci ya jawo min kenan "

Wallahi a cikin motan duk wanda na juya kowa kuka yake yi, aka yi ta bata hakuri, da yi mata nasiha, kafin ta dawo hayyacinta. 

Shin Sallah kadai ce abinda addinin Islama ya ce mu yi? Shin Sallah ne kadai hakkin Allah akanmu? Shin Sallah ce kadai hakki tsakanin Musulmi da Musulmi?  Wallahi wannan babban kalubale ne akan kowane Musulmi, Wallahi idan ta yi ridda to tabbas mu sani Allah ba zai kyale dukkanin wanda ke da hannu a cikin wannan al'amari ba, da shi Mijintan,  da Iyayensa, da mu 'yan motar, kai har ma wanda ya karanta, tana da hakkin akanka koda kuwa na addu 'a ne. 

Allah ya kyauta, ita kuma Allah ya fitar mata da mafita.
Raariya.

No comments:

Post a Comment