Wednesday, 3 October 2018

Lauyoyi 3 dake kare wadda ake zargi da kashe mijinta, Maryam Sanda sun barta a kotu sunce sun ajiye aikin kareta daga zargin

Manyan lauyiyi uku dake kare matar da ake zargi da kashe mijinta, Maryam Sanda sun ce sun daina, sun ajiye aikin kareta daga zargin da ake mata.


Ana zargin Maryam da kashe mijinta, Bilyaminu Halliru Bello wanda dane a guri shugaban PDP, Alhaji Bello Halliru Muhammad, ana kuma zargin mahaifiyar Maryam, Maimuna Aliyu, Aliyu Sanda, da kuma wata Sa'adiya da taimakawa Maryam din boye laifin da tayi ta hanyar goge jinin daga gurin da lamarin ya faru.

Daily Trust ta ruwaito cewa, lauyiyin uku sun bayyana ajiye aikin nasu ne ba tare da fadin dalilin yin hakan ba amma wakilinta ya samu ta wata majoya cewa rashin biyansu kudin aikine akan lokaci ya janyo haka.


No comments:

Post a Comment