Saturday, 20 October 2018

Lionel Messi ya bayar da tallafin Euro miliyan 30 domin yaƙar ciwon daji


Shahararren ɗan wasan ƙwallon Barcelona ta La Liga Lionel Messi ya kai ziyara mai muhimmanci inda ya bada gudunmowar gina kataɓaren asibitin magance ciwon daji.


Ɗaga daga cikin sanannun ƴan wasan kwallon a duniya wato Lionel Messi yana yawan bayar da gudunmowa domin ci gaban al'umma.

Dan wasan ƙwallon daga Ajantina ya halarci taron bayar da tallafi domin gina kataɓaren cibiyar magance ciwon daji.

Da yawan mutane sun shaidi Lionel Messi da yawan bayar da tallafi domin ci gaba al'umma.

A yayinda yake ziyara a asibitin magance ciwon daji mai suna Sant Joan de Deus ya gana da marasa lafiya matasa inda ya bayyana niyyarsa na ci gaba da bada tallafi domin kauda cutar. Daga bisani kuma ya bayyana farin cikinsa akan yadda ya samu damar taimakawa domin magance cutar.

Sanadiyar tallafin da kungiyar kwallon ƙafar Barcelona da Messi suka bayar har na Euro miliyan 30 ga cibiyar yaki da ciwon daji a ko wacce shekara ana warkar da yara fiye da 400.
TRThausa

No comments:

Post a Comment