Tuesday, 9 October 2018

Lokaci yayi da zan kasance tare da Real Madrid>>Hazard

Dan wasan gaba na Chelsea Eden Hazard ya sake haifar da shakku kan yiwuwar cigaba da zamansa a kungiyar, inda dan wasan yace har yanzu, yana son komawa Real Madrid, duk da irin bajintar da yake nunawa a Ingila bayan soma kakar wasa ta bana.


Hazard ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin da Chelsea ta samu a farkon kakar wasa ta bana kan dukkanin wasannin da ta buga ba tare da yin rashin nasara a koda wasa daya ba, wanda hakan ya baiwa kungiyar daman darewa saman teburin gasar Premier, tare da takwarorinta na Liverpool, da Manchester City.

Hazard dan kasar Belgium, ya zama dan wasa na biyu mafi kwazo a gasar cin kofin duniya da Rasha ta karbi bakunci, bayan jagorantar kasarsa zuwa matsayi na uku a gasar.

Cikin bayanin da Hazard yayi a baya bayan nan, dan wasan ya ce lokaci yayi da zai fuskanci sabon kalubale na komawa Real Madrid, kungiyar da ya dade yana muradin kasancewa tare da ita.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment