Wednesday, 24 October 2018

Mace me kamar maza: kalli yanda take aikin kanikanci

Wannan baiwar Allahn me suna Uzma Nawaz me shekaru 24 da ta fito daga kasar Pakistan ta baiwa mutane da dama mamaki yanda take aikin kanikanci dake bukatar karfi wanda yawanci maza aka sani da yinshi.Kamfanin Dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa Uzma na daga daga cikin mata na farko a kasar ta Pakistan da suka fara aikin kanikanci, ta kammala karatunta na digiri akan aikin injiniya, daga nan ne sai ta samu aiki da wani shagon gyaran motoci inda ta fara aiki, kamar yanda ta bayyana.

Tace halin talauci da iyalanta suke ciki ne yasa ta aikin kanikanci, kuma jama'a da yawa su kanyi mamaki idan suka ganta tana wannan aiki.

Lokaci zuwa lokaci dai a nan Najeriya muma mukan ga mata na aikin kanikanci wanda hakan ke rika baiwa mutane mamaki ashe dai ba a nan ne kadai muke da mata masu aikin kanikancin ba, saidai nasu a tsaftace kuma a zamanance ake yinshi.No comments:

Post a Comment