Monday, 8 October 2018

Mace ta biyu ta bayyana tana zargin Ronaldo da yi mata fyade

Ana tsaka da maganar matarnan 'yar kasar Amurka, Kathryn Mayorga da ke zargin tauraron dan kwallon kafar Juventus, Cristiano Ronaldo da yi mata fyade sai ga wata matar itama ta bayyana tana zargin dan wasan da fyade.


Lauyan dake kare matar ta farko ne ya bayyanawa 'yansanda haka inda yace wata mata ta sameshi inda ta bayyana mai cewa itama Ronaldon ya mata fyade, kamar yanda Daily Mail ta ruwaito.

Ronaldo dai na neman shiga cikin matsala tun zargin farko da aka mishi inda wasu suka sokeshi wasu kuwa suka yabeshi, wannan zargi har yana neman taba yarjejeniyar talla da yake wa kamfanin kaya na NIKE na miliyoyin daloli.

Yanzu kuma ga wannan.

No comments:

Post a Comment