Friday, 26 October 2018

Mace ta farko ta zama Shugabar Kasa a Itopiya

Bayan ba wa mata kaso hamsin cikin dari na kujerun Ministocin gwamnatin Itopiya, a yanzu kuma an zabi mace a matsayin Shugabar Kasar.


Majalisar Tarayya ta Itopiya da ta Wakilan Jama'a sun gudanar da zama na hadin gwiwa a Addis Ababa inda suka amince da murabus din Mulatu Teshome bayan kwashe shekaru 5 yana shugabancin Kasar kuma suka maye gurbinsa bayan jefa kuri'a da masaniyar harkokin diplomasiyya Sahle-Work Zewde.

Tun watan Yuni Zewde na aiki a matsayin Wakiliyar Musamman ta Majalisar Dinkin Duniya a Tarayyar Afirka.

A baya ma Zewde ta taba zama jakadiyar ıtopiya a kasashen Sanagali Djibouti da Faransa. inda ta yi aiki a cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya da dama.

A makon da ya gabata Firaministan Itopiya Abiy Ahmad ya bayyana cewa, ya bayar da amanar rabin kujerun Ministoci ga mata.

Bayan kowanne shekaru 6 ne Majalisar Dokoki ta ke zabar Shugaban Kasar mara cikakken iko.

Teshome ya zama Shugaban Kasar ıtopiya a shekarar 2013 lokacin yana matsayin jakadan kasar a Turkiyya inda Majalisar Dokoki ta zabe shi.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment