Monday, 29 October 2018

Madrid sun daina Darajani shi yasa na barsu>>Ronaldo

Tauraron dan wasan kwallon kafa na Juventus, Cristiano Ronaldo a karin farko ya bayyana dalilin da yasa ya bar kungiyar Real Madrid zuwa Juventus.

Da yake hira da jaridar France Football, Ronaldo ya bayyana cewa, ya bar Real Madrid ne saboda irin yanda suke darajashi ya canja ba kamar a shekaru biyar zuwa shida na farkon zuwanshi kungiyarba.

Yace irin kallon da suke mishi ya zama kamar basu darajashi. Shugaban kungiyar yana min kallon ko na tafi fa ba abinda zai faru, ba za mu samu matsala ba, injishi.

Ronaldo yace bawai Perez ba ya sonshi bane amma yanda yake nuna mishi ko da shi ko bashi Madrid ba zata samu matsala ba shi yasa shi kuma ya tafi, ya kara da cewa ba wai dan kudi yaje Juve ba, da kudi yake so da sai ya tafi China inda zai samu ninki 5 na kudin da Madrid da Juve suke biyanshi amma yazo Juve ne saboda sun nuna suna sonshi kuma suna darajashi.

Akan maganar cin gasar Ballon d'Or kuwa, Ronaldo yace yana son ya cinye wannan kyautar ta zama ta shida, ya shiga gaban Messi, yace ya cancanci cin kyautar ta bana.

Akan maganar zargin fyade kuwa Ronaldo yace shi ya san kanshi kuma yasan abinda yayi yasan abinda bai yi ba amma ya tabbata gaskiya zata yi halinta kuma masu son su bata mishi suna zasu gani.

Ya kara da cewa ya yiwa budurwarshi bayani amma danshi ba zai fahimci komai ba, ya kara da cewa 'yar uwarshi da mahaifiyarshine suka fi nuna bacin rai sosai akan wannan lamari, be taba ganin bacin ransu irin wannan karin ba.

No comments:

Post a Comment