Saturday, 6 October 2018

MAGANAR GASKIYA APC NA KAKABAWA TALAKAWA 'YAN TAKARAR DA BA ZABIN SU BA

Hada kai da ake yi tsakanin Shugabannin Jam'iyyar APC da Mahukunta ana muzguna wa Talakawa wajen gudanar da zabukan fitar da Gwani na 'Yan Takarkaru babu Adalci a ciki. 


Ana saka Son Zuciya aciki, a maimakon a ba wa al'umma dama su yi nasu zabin. Sai dai a zabar musu Dole, ko da kuwa ace ba su gamsu da Nagartar sa ba. Hakika hakan ba zai taba Haifarwa da Jam'iyyar 'Da mai Ido ba.

Ban da ma hawan 'kawara da ake yiwa Dimukuradiyya Ina Ruwan Gwamna da saka Baki cikin Zaben Sanatoci ko kuma na 'Yan Majalissun Wakilai na Tarayya ? 
Dama akwai wani Hurumi ko kuma aiki da ya hada Gwamna Da 'Yan Majalissu na wakilai ? 

Ire-Iren Wannan Rashin Adalcin Jihohi dai-dai ne suka tsira ba'a yi musu shi ba a kasar nan.

To Magana Ta Gaskiya kuma ta 'Karshe ita ce, Babu Sauran Sak, Cancanta za mu Duba a kowanne Mataki domin Zabawa Al'ummar mu Wakilai Nagari da suka dace a kowacce Jam'iyya Su ke.
Rariya.

No comments:

Post a Comment