Friday, 19 October 2018

Majalisar Kano ta gayyaci Jafar Jafar kan bidiyon Ganduje

Majalisar Dokokin jihar Kano ta gayyaci editan kafar yada labarai ta Daily Nigerian Jafar Jafar game da bidiyon da ya wallafa wanda ke ikirarin nuna Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje na "karbar cin hanci" daga hannun wasu 'yan kwangila.

An gayyaci mawallafin jaridar ne don ya ba da ba'asi a gaban kwamitin da majalisar ta kafa don binciken bidiyon.

BBC ta tuntubi dan jaridar kuma ya tabbatar mata da cewa ya samu kwafin takardar gayyatar.
"Duka zaman kwamitin za a yi shi ne a bainar jama'a... kuma wata dama ce ta fito da karin hujjoji da yin tambayoyi," in ji takardar gayyatar.

A makon da ya gabata ne jaridar Daily Nigerian da ke wallafa labaranta a intanet ta saki labarin da ke cewa wani gwamna a yankin arewa maso yammacin kasar wanda ke neman zarcewa a mulki karo na biyu, yana karbar makudan kudade a wajen wasu 'yan kwangila.
Sai dai gwamnan ya musanta wannan zargi.

Har ila yau a ranar Lahadi ne jaridar ta saki bidiyo na farko daga cikin kusan 15 da ya ce yana da su, a shafin jaridar tasa.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment