Thursday, 18 October 2018

Majalisar tarayya ta hana bankuna cirewa mutane kudin kula da ATM

Majalisar dattijai a zamanta na jiya ta yi dokar da ta hana cirewa mutane kudin kula da katin ATM da bankuna ke yi, kakakin majalisar, Bukola Saraki ne ya bayyana haka.


Saraki ya ce, lokacin yana aiki da ma'aikata me zaman kanta shine ya fara shigo da na'urar cire kudi ta ATM Najeriya, yace, daga wancan lokaci zuwa yanzu ya kamata ace an daina karbarwa  mutane kudi akan katin ATM din.

Yace, sun baiwa babban bankin Najeriya umarnin sanya wannan doka cikin aiki nan bada dewa ba domin dama dan jama'a suke aikinsu.

No comments:

Post a Comment