Thursday, 4 October 2018

Manyan kamfanonin da Ronaldo kewa talla sun nuna damuwa akan zargin fyaden da ake mishi: Ba zai rika bugawa kasashi wasa ba: Ya gogawa matar ciwon da ake dauka wajan saduwa: Juventus sunce har yanzu suna tare dashi

Idan ba'ayi hankali ba lamura zasu fara cabewa Ronaldo bayan da wata mata 'yar kasar Amurka ta fito ta bayyana cewa ya mata fyade a shekarar 2009.


Yanzu dai babban kamfanin dake yin kaya na NIKE wanda Ronaldon ya kwashe shekaru 15 yana musu talla sun nuna damuwa akan zargin da akewa Ronaldo inda a cikin wata sanarwa da suka fitar yau Alhamis sun ce zasu rika bibiyar labarin na zargin Ronaldo da fyade sau da kafa, kamar yanda Sky ta ruwaito.

Haka kuma kamfaninnan dake yin wasan Game na Kwamfuta, watau EA Sports wanda shima Ronaldon na musu talla sun bayyana damuwa akan wannan lamari inda suka ce ba zasu so wani dan wasa dake musu tallaba ya aikata abinda be kamata ba, dan haka suma zasu bi lamarin sau da kafa su ga yanda za'a kare.

A wani lamari da shima ba na dadi bane akan Ronaldon kasarshi ta Portugal ta bayyana cewa ba zai buga mata wasannin cin kofin nahiyar turai ba da kuma dukkanin wasu wasannin sada zumunta da za'a buga nan gaba.

Kasar ta bayyana cewa,  an yanke wannan hukunci ne tare da Ronaldon da shugaban hukumar kwallon kasar da kuma me horas da kungiyar kwallon kasar.

Haka kuma dai lauyan matar da ta zargi Ronaldo da yin fyade ya bayyana cewa tun lokacin da lamarin ya faru a shekarar 2009, wadda yake karewa din tayi ta fama da takaici sannan kuma Ronaldon ya goga mata ciwon da ake dauka na hanyar saduwa.

Saidai duk da wannan chakwakiya dake faruwa akan Ronaldon, sabuwar kungiyarshi ta Juventus ta tsaya kai da fata cewa dan wasan nata ya nuna jajircewa da kuma iya aiki wanda duk wani dake kungiyar ya yaba dashi.

Dan haka wannan zargi da ake mai na wani abu da ya faru kusan shekaru 10 da suka gabata ba zai canja irin kallon da suke wa Ronaldon ba.

No comments:

Post a Comment