Saturday, 20 October 2018

Masallacin da aka shekara 37 ana kallon alkibla ba dai-dai ba

Wani limami ya gano wani masallaci a Turkiyya wanda aka shafe sama da shekara 37 ana sallah amma kuma ba dai-dai ake kallon alkibla ba.


Masu bauta a masallacin su kusa shekara 40 suna kallon wajen da ba alkibla ba suna sallah.

Rahotanni sun ce masallacin wanda a Sugoren da ke yammacin kasar ta Turkiyya, an gina shi ba dai-dai ba tun a shekarar 1981.

Sabon limamin wanda bai fi wuce shekara 24 da hudu da haihuwa ba Imam Isa Kaya, ya gano cewa alkiblar masallacin ba dai-dai ta ke ba, hakan ya sa ya gana da manyan malaman addinin musulunci da kuma shugabannin yankin don sanar da su cewa akwai matsala a wajen yadda ake kallon alkibla a yayin sallah a masallacin.

Daga karshe an gano cewa tun a farkon ginin masallacin ne aka samu kuskure wajen dai-daita alkiblar.

Gabas ake kalla idan za a yi sallah, wanda ake ganin shi ne saitin dakin ka'aba da ke Makka a kasar Saudi Arabia.

Yanzu dai sabon limamin, ya yi amfani da wani farin kyalle inda ya yi shaidar alkibla, domin a rinka kallon can idan za a yi sallah a masallacin.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment