Sunday, 21 October 2018

Masu garkuwa da Mohammed Dewji, matashin da yafi kowa kudi a Afrika, sun sallame shi

A Tanzania masu garkuwa da Mohammed Dewji sun sallame shi bayan da ya share kusan kwanaki 9 a hannun su.


Sallamar dake zuwa bayan da masu bincike dangane da sace atajirin Mohammed Dewji ranar 11 ga watan Oktoban nan da muke cikin sa suka sanar da gano direban dake tuka motar da aka yi awon gaba da hamshakin mai kudin .

A baya dai iyalan Mohammed Dewji sun sanar da ware rabbi milyan na dalla ga duk wanda zai iya taimakawa domin gano ida yake yanzu haka.

Shugaban yan Sanda na Tanzania Simon Sirro a wata ganawa da manema labarai a Dar Es Salaam ya bayyana cewa sun samu nasarar gano direban motar, ,da mai motar, da aka shigo Tanzania da ita ranar 1 ga watan Satumba daga wata kasa dake iyaka da Tanzania.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment