Monday, 15 October 2018

Matasa Sun Fara Tattaki Daga Bauchi Zuwa Adamawa Domin Atiku

Wasu ayarin matasa sun sha alwashin tattaka wa aka kasa daga jihar Bauchi zuwa jihar Adamawa domin nuna wa Atiku Abubakar goyon baya da kuma yi masa fatan zama shugaban kasar Nijeriya a babban zaben 2019 da ke tafe.


Wakilinmu na Bauchi, ya shaida mana cewar, masu tattakin sun fara yin wannan tattakin ne tun a ranar Larabar nan, inda suka tashi daga jihar Bauchi da misalin karfe sha biyu na rana, hadi da kwasan titin Adamawa a kar.

Manema labaru sun nemi jin ta bakinsu dangane da daukan wannan matakin, inda suka shaida cewar sun himmatu wajen yin wannan tattakin ne domin tabbatar da cewar shugaban kasar Nijeriya ya fito daga shiyyar Arewa Maso Gabas a wannan lokacin.

Hassan Mahmud Hassan shi ne jagoran masu tattakin nuna goyon bayan Atikun, ya shaida cewar idan shiyyar Arewa Maso Gabas ta samu shugaban kasa za a samu ci gaba wajen shawo kan matsalolin da suke addabar shiyyar kamar na tsaro da rashin samun ababen more rayuwa ga yankin, kana ya shaida cewar dan shiyyar ne kadai zai iya kawo karshen wannan matsalolin da Arewa maso Gabas ke fuskanta.

Yake cewa, “ni ne na tsara wannan tafiyar tattakin daga Bauchi zuwa Adamawa. Dalilinmu na yin hakan shi ne tun da aka dawo siyasar demorakdiyya, shiyyar Arewa maso Gabas ba a taba bamu dama ba, kuma mune yankin da muka zama koma baya kan ci gaba a wannan kasar.

“Don haka ne ya sanya tun da muka ci sa’a muka samu dan takarar shugaban kasa a wannan yankin Arewa maso Gabas muna tsammanin zai kawo mana canji mai sunan canji da ci gaba mai sunan ci gaba a wannan yankin namu. Sannan, muna da tabbacin zai yi kokarin shawo kan matsalolin da suke addabarmu na tashin hankula da kashe-kashe da suke addabar yanki,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “Mun yi imanin cewar dan wannan shiyyar shi ne kawai zai iya tsayin da ka ya tabbatar ya shawo kan dukkanin matsalolin tsaro da suke addabar wannan yankin; a dukkanin Nijeriya, shiyyar Arewa Maso Gabas ne kadai bata da hanya tagwaye daga jiha zuwa jiha, kuma ba mu da wasu ababen da suke kawo mana ci gaba a wannan yankin don haka muka tashi tsaye domin tabbatar da cewar Wazirin Adama, Alhaji Atiku ya samu nasarar kasancewa shugaban kasa domin ya samu zarafin kawo mana ci gaba da kasa baki daya,” Inji shi

Dangane da wannan tattakin da suka fara yinsa kuwa, Hassan Mahmud Hassan ya shaida cewar sun dauki wannan matakin ne domin nuna wa duniya tsananin bukatarsu na samun shugaban kasa a wannan shiyar, suna masu shaida cewar su babbar damuwarsu a wannan lokacin shine a samu dan arewa maso gabas da zai mulki kasar nan domin su samu zarafin kyautata rayuwar.

Ya kara da cewa, ba sun yi wannan tattakin domin siyasa ba ne, illa dai sun yi hakan domin ci gaban shiyyar ta Arewa maso gabas, ya kuma shaida cewar adalci shine a baiwa wa wannan shiyyar zarafin mulkan kasar nan.

Ya shaida cewar za su ke wannan tafiya suna yada zango a wuraren da suka gaji, inda ya shaida cewar sun tanadi guzuri da kayyakin amfaninsu har su samu isa can jihar ta Adamawa domin nuna wa Atiku kauna da soyayya.

Hassan ya kuma bayyana cewar sun sanar da jami’an tsaron da abun ya shafa domin samun izini da tsaro, “mun tanadi abun da za mu ci a hanya da magunguna idan Allah ya sanya wani ya samu rashin lafiya a cikinmu. Dangane da hidimar tsaro, mun nemi izini daga shugaban ‘yan sanda, Darakta SSS, da shugaban sojoji dukkaninsu mun samu izini daga wajensu,” in ji Hassan

Ya shaida cewar za su shafe tsawon kwana hudu idan Allah ya sanya suka samu isa a cikin wannan kwanakin, idan kuma basu samu isa ba za su kara wasu kwanaki amma ya tabbatar da cewar za su isa wannan jihar ta Adamawa ne a kafa, “Mun fara tsara wannan tattakin tun lokacin da aka tsaida Atiku neman shugabancin Nijeriya a karkashin PDP. Amma neman izini daga jami’an tsaro ne ya dan sanya bamu samu kammala shirye-shiryenmu da wuri ba. mun samun amincewa yanzu mun fara wannan tattakin, daga nan Bauchi sai Adamawa,” Inji shi


Rariya.

No comments:

Post a Comment