Tuesday, 30 October 2018

Mawakin Hausa, Saeed Nagudu, dan gani kashenin Buhari ya koma bayan Atiku

Tauraron mawakin Hausa, Saeed Nagudu wanda a kwanakin baya yana daya daga cikin masu goyon bayan gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a yanzu ya koma bayan Atiku.


A lokuta da dama munji Saeed Nagudu na yabon Buhari ko kuma yana kare tsare-tsaren gwamnatinshi, misali a lokacin da akai ta yayata maganar cewa shugaba Buhari ya cewa matasan Najeriya cima zaune, Saeed Nagudu na daga cikin wanda suka kareshi, danna nan dan karanta abinda yace

Haka kuma a lokacin da hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ramalan Yaro har shehin malamin addinin Islama, Dr. Ahmad Gumi ya fito yana caccakar gwamnatin Buhari, Saeed Nagudu na daya daga cikin wanda suka mayarwa da malamin martani, danna nan dan karanta abinda yace akan wannan lamari

Saidai a yanzu Saeed Nagudu ya fara saka hotuna da labaran dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar inda wasu har sun fara tambayarshi ya bar Buharinne?

Dama dai masu iya magana na cewa babu abokin dindin din ko makiyin dindindin a siyasa.


No comments:

Post a Comment