Monday, 8 October 2018

Mbappe ya kafa tarihin da rabon da a samu irinshi tun shekaru 45 da suka gabata a League 1

Tauraron matashin dan kwallon PSG, Kylian Mbappe ya ciwa kungiyarshi kwallaye 4 a wasan da suka buga da Lyon jiya.


Neymar ne ya fara ciwa PSG din kwallo a bugun daga kai sai gola da suka samu, sai kuma ana minti 61 da wasa, Mbappe ya fara zura kwallaye har sai da ya ci sau 4.

Wannan bajinta da yayi tasa ya kafa tarihin kasancewa dan kwallo mafi karancin shekaru da ya taba cin kwallaye 4 a wasa daya a gasar League 1 ta kasar Faransa cikin shekaru 45 da suka gabata.

Da yake hira da manema labari, Mbappe yace ya kamata ace yaci kwallaye fiye da haka amma dama haka kwallo ta gada.

Shima abokin aikinshi, Neymar da yake magana akan wannan bajinta da Mbappe yayi yace duk da karancin shekarun shi amma suna sauraronshi idan yayi magana a kunyar kuma yana daya daga cikin wanda suke bayar da sakamakon da ake bukata.

Neymar ya kara da cewa danshi na matukar son Mbappe.

No comments:

Post a Comment